Ganin jini ga mace me juna biyu.
A WATAN 1 ZUWA NA 3
Akan iya ganin jini gamace me juna biyu haka dan kadan kuma baiyi kama da jinin al'adaba hakan ba matsala bane musamman ma a watannin farko.
amma idan jinin dayawa yake zuba hade da ciwon mara ko babu to wannan ba makawa alamace ta bari wato cikin zai iya lalacewa.
ZUBAR JINI A WATANNI 4 ZUWA NA 6
shima alamace dake nuna akwai matsala
kamar ace girman da ba acikin ma haifaba kokumama ba dabane acikin wata tsokace take girma kamar da .
Atakaice dai ganin jini ga mace me juna biyu idan kadanne watakilama hade da yar majina awatannin farko hakan ba abun damuwa bane amma in yana zuba dayawa kamar zuwan na al ada koda ba kalar su dayaba hakan akwai BARAZANAR SAMUWAR BARI.
WASU MATSALOLIN DA SUKE ZUWA TARE DA JINI GA MACE ME JUNA BIYU DAKE BUKATAR TAI MAKON GAGGAWA,
* CIWAN MARA HADE DA ZUBAR JINI SOSAI
* MATSANANCIN AMAI DA TASHIN ZUCIYA
* DUSHASHEWAR GANI
* matsanancin zazzabi
* suma
* ciwan qugu matsananci
*ciwan baya matsananci
* azababbiyar gajiya marar tafiya
DAZARAR ANGA WADANNAN ALAMOMIN AI MAZA AJE ASIBITI DUKKAN SU ALAMOMINE NA BABBAR MATSALA KAMAR
* KAMUWA DA KWAYOYIN CUTA
* ALAMOMIN BARI
* GIRMA DA A WAJEN MA HAIFA
* KOKUWA GIRMAN TSOKA MAIMAKON DAN MUTUM
dukkan su na zuwa da zubar jini game juna biyu.
Danhaka yan uwa in anga alamun haka sai aimaza aje asibiti.
ALLAH YA SAUWAKE


