DANYIN TAMBAYA KO NEMAN SHAWARA ZABI GIDA DAYA KA SHIGA A NAN KASA
HOMEZAMAN AUREJAVA|HTML CODE

ADDINISOYAYYALAFIYA
Joint our WhatsApp Group

nan
12026-04-10
*Post reply · Invite friends · From end
Abdul adamu sani wudil LAFIYA UWAR JIKI.

hakika lafiya tana daya daga cikin manyan ni'imomi da Allah swt yayiwa dan adam bayan ni'ima ta addinin musulunci da imani. Dukkan wanda Allah swt yabawa lafiya haqiqa Allah yabashi babban jari dukkan wanda Allah swt ya jarraba da rashin lafiya to tabbas Allah swt ya jarrabeshi da babbar jarabawa daga cikin jarrabawa masu girma.

* da lafiyane ake samun damar yin komai na rayuwa kama daga kan ibada ,neman kudi ,cin abunci ,samun farinciki dashauaran su,kwanciyar hankalin mai gida da iyalan sa.

Rashin lafiya na daya daga cikin jarrabawa dake jefa rayuwan dan adam acikin tashin hankali da qunci na rayuwa dan adam yakan jishi kamar a kurkuku.

Lallai kenan lafiya na buqatar a bata kulawa ta musamman dan haka naga yadace nakawo hanyo yin kula da lafiya .


ALLAH SWT YAFADAMA NA A ALKUR'ANI CEWA ZaI JARRABEMU DA ABUBUWA KALA KALA DAGA CIKI A KWAI JARRABAWA TA LAFIYA.

Manzon rahama s.a.w yakecewa dukkan wani mutum da Allah swt yajarrabeshi da watata masifa ko rashin lafiya ne koda qaya yataka sai yai haquri bai dora laifin akan waniba yai tawakali ga Allah swt to Allah zai sanya ciwon yazama kaffara ne a gareshi yakuma bashi lada.

HANYOYIN KULA DA LAFIYAR

* yawaita addu'ah Allah swt yabamu lafiya ,yakuma karemu daga cututtuka.

*bin shawarwarin manzan Allah swt tahan yar yin addu'o i ,yayin aikata abubuwa, tsafta da shaura,

*yin amfani da magun gunan da annabin rahama s.a.w ya umarta kamar su zaitu,habbatul sauda,zuma,zamzam, da shauran su idan bukatar amfani dasu ya tashi,

* kada a aikata dukkan abubuwan da Annabin rahama s.a.w yace a bari kamar dakuma aikata abun daya umarta kamar cin abunci da hanun dama ,barin ci da hanun hagu, cin abunci a hankali lauma bayan lauma ,cin abunci dai dai musali ba a cika cikiba fal,da shauran su

SANNAN YANA DAGA HANYOYIN KULA DA LAFIYA

* cin abunci me kyau ,me gina jiki

*tsaftace jiki ,wanka akai akai, wanke tufafi

* kula da lafiyar haqora tahan yar kuskure baki, asuwaki, makilin da burushi ,kuskure baki bayan cin abunci dasake hakori in anci nama ko abu me yawa yawa duk dan kula da lafiyar jiki.

*samun wada taccen hutu kamar barci a qalla a kullum mutum yasmi awa 8 koda ba a lokaci daya ba.

* motsa jiki ,kamar wasa da iyalanka agida ,tafiyar qafa me dan nisa, aikin qarfi ba mai tsananiba lokaci lokaci da shauran su.

* cin abunci akan lokaci basai anji matsananciyar yunwaba. Koda kadan kadanne.

* tsaftace abunci da abunsha tahanyar killace shi ,kada a ci inyabaci ,kar abar kwarika su haukai kamar qudaje ,kyankyasai da shauran su. Shan ruwa mai kyau da tsafta ,in a qauye ne yana da kyau ana tafasa ruwa sai a ajiye a ma ajiyi me kyau adunga sha.

*tsaftace mahalli kamar share gida ,ban daki,kofar gida share juji da konashai a guri marar cutarwa,share yanar gida,kada abar shirgi shirge a gidaje marasa amfani da shauransu.

* abar shaye shayen taba ,giya ,ko zama kusa da maishan taba.

* kada kasha magani in baka da lafiya har sai ka tambayi likitanka koda qaramin zazzabine.

* kawar da dukkannin abubuwa da zasu iya kawa hatsari a gidaje kamar kusa,langa langa,kwalba ,fiya fiya, dan dayis,shantal ,da shauran su a guraren da yara zasu iya dauka ko suyi kara dasu.

*kula da lafiyar yaran gida da abubuwan wasan su ,tsaftarsu,da guraren wasan su da shauran su.

* kwana a cikin ragar sauro ko kore sauro daga mahallinmu tahanyar tsaftace shi

* idan anji alamaun rashin lafiya ayi gaggawar zuwa asubuti dan ganin likita yabada shawara

* kiyaye amfani da magungunan gargajiya barkatai

* kiyaye kunnuwa daga qarar abubuwa kamar sauti me qarfi na waqoqi,ko mota

*kiyaye ido daga abubuwan cutarwa kamar hayaqi ,kyamikal ,kar asa komai a ido sai da izinin dakta

*kula da iyali tahanyar samu su farinciki , ma aurata sukiyaye junansu tahanyar kadaituwa da juna ta buqatar aure.

*mallakar kayan amfani na musamman kamar kayan yankan farce,sosan wanka.

* hana yara zirga zirga daf da magariba da shauransu.

*yin amfani da dukkan shawar warin da dakta yabaka .

*
kashe wuta yayin bacci,kula da wayarin din gida in ya lalace a gyara kar ana barin waya a waje
Da shauran hanyoyin kara lafiyar dan adam

IN ALLAH SWT YA JARRABI MUTU DA RASHIN LAFIYA BAYAN YA YI IYA KOKARINSA WAJEN KIYAYEWA TO SAI YAYI HAQURI HAKAN NE ZAISA YASAMI LADA KUMA A KANKARE MASA ZUNUBANSA.

ALLAH YA KAREMU .

ZAMU CIGABA IN ALLAH YASO
2016-01-23 11:26 · Reply · (0)

Online: Guests: 1

2970031
HOMESpeedCounter.net - Free web counter
Share Button
© 2012 TO 2022 www.arewa2.wap.sh created by Abdul Adamu Sani Wudil
1
SAHEN LABARAN HAUSA
Aminiya
hausa radiyo
Almi'izan
hausa leadership
voa hausa
trt hausa
rfi hausa
dw hausa
bbchausa
cri hausa
A A
AIKO SAKOSMSKIRA© 2020 arewa2.wap.sh
call 07033031695

l
sss

XtGem Forum catalog