Abdul adamu sani
MATSALOLIN DA SUKE SHAFAR ADDININ MUSULUNCI A YAU.
yan uwanan wannan ra'ayinane dafatan in anga kuskure a gyramin.
Zan yibayanine akan abubuwan da suka jefa addinin musulunci a mawuyacin hali suka zama sunsahi a kurkuku sunyimasa tarnaqi ,
*har a yau wasu musulmai suke gani kamar addinin ma qaryane .
*wasu kuma suke ganin addinin ma yatakuramu su ya hanasu sakat ya hanasu walawa da sheqe ayarsu.
*wasu kuma suke goyan bayan yahudu da nasara.
1, MUNANAN AL'ADU:
al ada marar kyau tabada gudummawa me tarin yawa wajen rusa tsarurruka na addinin musunluci ,
ba abunda da yake hana mutane aiki da ilminsu a yau irin al'ada musamman a qasar hausa malami zakaga a unguwa yakaranta littafai na addini kamar irin su iziyya risala ahlari kuma yana karantar wa AMMA HAKAN BAI HANA SHI SABAWA AL'ADUN GARIN SU MUNANABA hasalima shine zakaga yake dora mutane akai kamar a guraren biki harkar mutuwa tare da cewa yasan hakan yasabawa addini.
2 secularism wato raba addini da siyasa.
Secularism shima wan bala'ine da yake cutar da addini.
Wato siyasa ,harkokin gwamnati a rabasu da addini .
Ace bazaka nuna addinin kaba ko aqidar ka ba agun aikin gwamnati ko makaranta a a sai dai ka ajiye aqidarka kayiwa qasa aiki indai ta sabawa dokar ma aikatar .MASU WANNAN RA'AYIN BARUWANSU DA TSARIN ADDINI A HARKARKASUWANCIN SU ,SUNA CIN RIBA SUNA BADA ITA ,BARUWANSU DA ADDINI A HARKAR RAYUWARSU .SU ABUNDA SUKA DAUKA ADDINI SHINE KAWAI KASHIGA MASALLACI KAYI SALLAH IN LOKACI YAYI AMMA BA RUWANSU DA DUKKAN WANI HANI KO UMARNIN ADDINI AHARKOKIN SU NA RAYUWA DA MU'AMALA DA KASUWANCI DA SHAURANSU.
wannan aqidar ta cutar da addini sosai a qasashen turawa musulma HATTA ANAN NAJERIYA DAYAWAN YAN SIYASA DA YANBOKO suntasirantu da dabi'un secularism batare da sun sani ba.
3, kwansutushin:
shinema qashin baya wajen rusa addinin musulunci sakamakon mafiya akasarin dokokin sa suna fada da dokokin musulunci .KUMA SUNA BARAZANA GARESHI.
Musali a kwansutushi bai yadda dukkan wani littafi dayake da wata dokoba tayi aiki sai in bata cikaro dashiba amma intaci karo dashi to dole a jiyeta ayi aiki dai ita. Sannan kwansutushin na daya daga abun da yasarqafe shari'ar Allah swt yahanata sakewa.
4 yan boko marasa tarbiyya/ko marasa ilmin addini ingantacce.
Dayawa yanboko musulmai marasa tarbiyya tagari ko mara ilmin addini SUNZAMA WASU MAKAMAI DA AKE AMFANI DA SU AKE RUSA ADDININ AKE YAQAR MUSULUNCI DASHI .su aganin su imma musulunci ahakan aiki sukemasa koka jisuke a ransu qaryane kawai bata lokacine yin addinin ma ,
5*MUNANAN MALAMAI:
suma sunbada gudummawa wajen jefa addinin musulunci a halin marar kyau ,kamar bada fatawar qarya, yada bokanci da sihiri da kauce hanya Allah swt amma suna canjamusu suna tahanyar dasuke rudar mutane kamar TSAFI SAI SUCE ASIRI KO TAIMAKO, SIHIRI SAI SUCE TAMBAYA DA SHAURAN SU,WASU KUMA SUNA BADA FATAWA YADDA ZATA DACE DA RA AYIN ME TAMBAYA DAN SUSAMI ABUN HANNUNSA.
6*TAQALIDANCIN /JAHILCI
dayawan mutane suna aikata abu ba daidaiba amma saboda malamansu ne suka koyamusu basajin komai a ransu .haka suma malaman .wato in ance taqalidanci ana nufin kafewa akan ra ayin malami dan shi me ilmine ko ma kamancin hakan .
Sautari zakaga malami yana aikata barna amma maimakon almajiransa sugujeshi ko subar wannan ra'ayin nasa saikaga sunyi shuru suna ma aikatawa .LAIFIN TAQALIDANCI SHINE IN MALAMI YANA KAN WATA FATAWA DATA SABAWA GASKIYA KUMA GA DALILI AMMA SAI AQI AMUNCEWA DA A SABAMASA.
7* MATSANANCIN KISHIN ADDININ MUSULUNCI BATARE DA ANFAHIMCESHIBA SHI ADDINI.
wanan matsalace babba wacce ta haifarwa da musulunci matsaloli marasa adadi tahaddasa mutuwar mutane milliyoyi ,tahanyar samar da yan ta adda a musulunci masu kafurta musulmai da tsokano wadanda ba musulmaiba bisa gurguwar fahimtarsu data sabawa qur'ani da sunnah.
Mafiya akasarin dariqu dasukai yawa a addini kamar su shi'a ,khawrij SUNSAMUNE SAKAMAKON KISHIN ADDINI TAREDA QARANCIN SANIN MEYE ADDININ.
7*SIYASAR DEMOKURADIYA:
a yau ba wani qalubale da barazana ga musulunci irin demokuradiyya .itace tushe da asali na wargatsa musulunci a qarqashin demokuradiyya
an amunce kowa yafadi ra ayinsa
, kowa yabautawa abunda yakeso kowanna gari su tsarawa kansu dokoki ,anbawa yanluwadi, karuwai da masu cin namam mutane ,auren jinsu dokar yara yancin mata DUKKAN WANI SHARRI A YAU YANA QARQASHIN TUTAR DEMUKURADIYYA.
8*MAQIYA DA MAGAUTA:
suma wadannan sunabada gudummawa wajen ruguza musulunci AKWAI MAQIYAN WAJE WATO YAHUDU DA NASARA DA ARNA ,MAQIYAN CIKI KUWA SUNE MASU TSAFI ,BOKANCI SIDDABARU DA SHAURAN AIKIN SHIRKA.
suma wadannan suna ta fada da addinin Allah swt A yau da zakace kai zakayi irin addinin da annabi yayi to saikayi fada dasu wato yahudu ,nasara matsafa,yan tsibbu ,yan addinin gargajiya ,da shauran su.
9*WASU SARAKUNA DA MASU MUQAMAI.
10*JAHILCI .
Anan zan dakata muna fatan Allah swt ya taimaki musulunci da musulmai ya karya dukkannin maqiyan musulunci in ba masu shirruwaneba. Wslm
daga
07033031695


